Gwamnan Jahar Borno Ya Yabawa Shugaba Buhari

Gwamnan jihar Borno ya yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari saboda kokarinsa a kan jihar Borno.

Gwamna Babagana Zulum, ya ce Buhari ya yi gaggawar sakin kudin da jiharsa ta nema a wurinsa.

Ta nemi kudade ne don ginawa ‘yan gudun hijira miliyan 1.7 gidaje 10,000, wanda yanzu haka an gama Gwamnan.

jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi wata magana yayin da yake zagaye anguwannin gidajen ‘yan gudun hijira 1000 a waje-wajen jihar.

Inda yace kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar don gina gidaje 10,000 na a kalla ‘yan gudun hijira miliyan 1.7 da ya kamata a ce sun koma anguwanninsu.

‘Yan gudun hijiran da suka dawo yanzu haka sun yada zango ne a sansanin gudun hijira da ke Maiduguri, Dikwa, Monguno, Dolori da kuma wasu anguwanni masu makwabtaka da kasar Kamaru.

Zulum ya ce gwamnatin jiharsa ta nemi kudi daga hannun gwamnatin tarayya, a kan ginawa masu gudun hijira gidaje, kuma an basu, The Punch ta wallafa.

Gwamnan, ya yaba wa shugaba Muhammadu Buhari a kan kokarinsa da jajircewarsa a kan sakin kudin gine-ginen gidajen ‘yan gudun hijira miliyan 1.7, wadanda ‘yan boko haram suka lalata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here