Ƴan Najeriya na ji a Jika – Jigon APC ga Tinubu

 

Jihar Osun – Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara.

Olatunbosun Oyintiloye ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta cire ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da suke ciki.

“Ƴan Najeriya na ji a jika”, jigon APC

Jaridar The Punch ta rahoto jigon na APC ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a birnin Osogbo babban birnin jihar Osun.

Olatunbosun Oyintiloye ya nuna cewa ƴan Najeriya na shan wuya wanda hakan ya sanya dole shugaban ƙasan ya ɗauki matakan kawo musu ɗauki, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Wace shawara aka ba Tinubu

Duk da ya nuna ƙwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai iya rage wahalun da ƴan Najeriya ke sha, ya ba da shawarar cewa ya kamata a bi hanyoyin da za su tabbatar da hakan cikin gaggawa.

“Ko tantama babu cewa shugaban ƙasa yana bakin ƙoƙarinsa domin rage raɗaɗin da ake fama da shi, amma ya kamata a bi hanyar da za a cimma hakan cikin sauri.”

“Ya kamata shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa an cire duk wasu abubuwan da suka kawo jinkiri wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani talakawa.”

“Matsalar tattalin arziƙin da mutane ke fuskanta ta yi tsanani a halin yanzu, dole ne shugaban ƙasa ya ɗauki mataki cikin gaggawa.

– Olatunbosun Oyintiloye

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here