Ba Bacci: Abubuwa Game da ‘Yan Najeriya ta Farko da ta Jera Kwana 4 Tana Girki
‘Yar kasuwa kuma kuku a Najeriya, Hilda Baci ta na kokarin kafa tarihi na wadda tafi kowa dadewa tana girki a duniya.
Tata Tondon ‘yar kasar Indiya ce take rike da kambun bayan da ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45 a shekarar 2019 tana girki.
Ana tsammani Hilda za ta shafe kwanaki 4 tana girki wanda akalla zai kai sa’o’i 90 kuma ba bacci har tsawon kwanakin.
Jihar Lagos – Wata ‘yar kasuwa kuma kuku a Najeriya, Hilda Baci mai shekaru 27 a yanzu haka tana kokarin kafa tarihi na ‘Guinness World Records’ bayan ta dauki mafi tsawon lokaci ta na girki.
Abubuwan da ya kamata kusa ni game da Hilda Baci
Wacece Hilda?
Hilda wata mai shagon siyar da abinci ce kuma kuku ‘yar asalin jihar Akwa Ibom masu arzikin man fetur daga Kudu maso Kudu.
Tana da wurin cin abinci a Lagos mai suna “My Food By Hilda”
Menene gasar kirki ta Guinness World Record ke yi?
Hilda Baci ta kai kwana 4 tana girki wanda zai kare a ranar Litinin 15 ga watan Mayu.
Wacce ke rike da kambun mafi tsawon yin girkin ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45.
Tata Tondon daga kasar Indiya ita ta kafa wannan tarihi a ranar 7 ga watan Satumba na shekarar 2019.
Read Also:
Baci tana dab da karya wannan tarihi saboda yanzu haka ta wuce sa’o’i 80 kuma tana neman kusan sa’a 19 ne kawai ta kafa sabon tarihi.
Me Hilda ke girkawa?
Hilda tana kokarin girka akalla kalolin abinci 35 da miya da sauran kayan makulashe, dukkansu abincin Najeriya ne wanda za a kira ‘yan uwa da abokan arziki su dandana.
Kalan abinci 35 da Hilda ke girkawa za a kammala su ne a cikin sa’o’i 90 saboda ta shiga jerin ‘yan Najeriya da suka kafa tarihi.
Wasu dokokin da Hilda za ta bi yayin wannan gasa?
Gasar girkin abincin wanda ke gudana a lambun Amore dake Lekki a cikin jihar Lagos, za a kammala shi ne tsakanin sa’o’i 90, cikin kwana 4, kuma ba bacci dare da rana safe da yamma har kwana 4.
Sai dai tana da mintuna 5 ko wace sa’a don hutawa, wata majiyar ta ce tana da mintuna 30 a sa’o’i 6 kuma akwai motar magani da za ta ke kula da lafiyarta, kamar yadda @abdullahayofel ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Su waye za su dandana abincin Hilda?
An ruwaito cewa an gayyaci mutanen da za su dandana abincin kyauta har na tsawon kwana 4, kuma an dauki nauyin komai na girkin abincin.
Jaridar Legit ta tattaro cewa dan wasan kwaikwayo na Nollywood Seyi Oluyole ya ziyarci wurin da ‘yan mata don su dandana abincin.
Shi ma gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya ziyarci wurin don dandana kalar abincin a ranar Lahadi 14 ga watan Mayu don kara mata karfin guiwa.