Rundunar ‘Yan Sanda ta Kama ƙaramin Yaron da ya Shirya Yadda za a yi Garkuwa da Shi

 

Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta samu nasarar cafke wani ƙaramin yaro wanda ya shirya yadda za a yi garkuwa da shi.

Yaron mai suna Ade Segun ya dai haɗa baki ne da abokansa guda biyu wajen shirya wannan aika-aikar.

Yaran da suka kitsa wannan shirin sun nemi iyayen Ade da su biya N20m a matsayin kuɗin fansa kafin su sako shi.

Jihar Delta – Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta bayyana cewa ta cafke wani ƙaramin yaro, mai suna Ade Segun, mai shekara 17 tare da abokansa, Precious da Nonso bisa laifin shirya yin garkuwa da shi na ƙarya da neman N20m daga wajen iyayensa.

New Telegraph ta tattaro cewa Segun tare da abokansa suna hannun ƴan sandan bisa hannun da suke da shi a wannan aika-aikar.

Iyayen Segun sun sanar da hedikwatar ƴan sandan jihar da ke Warri halin da ake ciki bayan sun samu labarin an sace mu su ɗa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Bright Edafe, ya bayyana cewa Segun ya shirya yadda za a yi garkuwa da shi ne, tare da abokansa domin ya samu N20m daga hannun iyayensa, a ranar 9 ga watan Mayu, 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Ya kuma bayyana cewa wata jami’ar ƴan sanda ce ta yi mu su shigo-shigo ba zurfi kamar za ta biya kuɗin, wanda a dalilin hakan ne aka yi ram da su.

A kalamansa:

“Wanda ake zargin, Ade Segun, ya shirya yadda za a yi garkuwa da shi tare abokansa biyu, Precious da Nonso, waɗanda suka kira iyayensa suka buƙaci su biya N20m a matsayin kuɗin fansa.”

“Iyayen sun kai rahoton lamarin wajen ƴan sanda a Warri, inda wata jami’ar ƴan sanda ta nuna mu su za a biya kuɗin fansar.”

“Lokacin da jami’an ƴan sanda suka isa wajen sun yi kwanton ɓauna kan ɗaya daga cikinsu, Precious wanda ya zo ɗaukar kuɗin, inda aka cafke shi.”

“Ya kai su inda Ade da ɗayan abokinsu suka ɓoye inda aka cafke su, sannan suka bayyana cewa su suka shirya komai.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here