‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50 a Jihar Neja

 

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 50 a wani kauyen da ke jihar Neja a tsakiyar Najeriya.

Jaridar Nation ta Najeriya ta rawaito cewa yankin da lamarin ya faru na yawaita fuskantar hare-hare da sace-sace domin neman kudin fansa.

Sannan a cewar rahotanni ‘yan bindigar sun kuma kwashe ababen hawan mutane da dabobbinsu.

Har yanzu dai ba a tabbatar da wannan hari a hukumance ba.

Amma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa abu ne da ya yi fice a arewacin Najeriya tun 2020, musamman Neja.

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa mutum 1,230 aka kashe a hare-haren ‘yan bindiga a watannin ukun farkon wannan shekarar a fadin Najeriya, sannan an sace 650.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here