Muzammil Mandawari
Tun ana gobe zaa gudanar da zaben na fuskanci zan iya rasa nasara a zaben, ganin yadda hukumar zabe INEC take fuskantar matsalolin isar da kayayyakin zabe a yankuna masu yawa dake kasar, ga kuma tarin wasu matsalolin a bangaren injin zaben da zaayi amfani dasu duk da haka na banyi tunanin dakatarwa ba don bawa Dimokaradiya cikekken yancin gudana a kasar…
Ban san yadda akayi hukumar zabe INEC ta iya samun nasarar kai dukkan kayan zabe zuwa yankunan Arewa gaba daya ba, ciki har da yankin Arewa maso gabas inda ake tashin hankali a lokacin, amma suka kasa samun nasarar kai cikakkun kayan zabe yankin kudancin kasar dayake da zaman lafiya sama da yankin Arewa maso gabas ba….
Dandalin Sadarwar Zamani Social Media ya cika da labarai na karya hotuna da bidiyoyi wadanda suka tayar da hankali hatta kasashen waje, dumin zarge zarge ne ake ta yadawa akan Gwamnatina ana cewa mun shirya magudi, ita kanta INEC tasan ba gaskiya bane maganganun amma duk da haka sukayi shiru ba tare da karyatawa ba…..
Na kasance cikin mamaki lokacin dana ziyarci Rumfar zabe a A bayelsa Mahaifata, amma sai naga wai duk da kasancewata shugaban kasar amma Injin zabe Card Reader ya kasa tantanceni, hakan ya kara firgitani na gansu da cewa tabbas INEC ta hada baki don ganin an kawar dani daga kan mulki, idan har ni shugaban kasa Card Reader bai tantance ni ba tayaya zai iya tantance ragowar mutanen dake jihar Bayelsa da sauran yankunan dake kudanci inda nafi yawan magoya baya, hatta mahaifiyata tare da matata duk Card Reader bai tantancesu ba haka muka hakura muka koma gida …..
Nasan tsayar da zabe a ranar zabe zai kasance kamar tayar da makamin Nuclear ne, musammam a yanayin da muke ciki wanda ake ta yada labarun karya a kasar da duniya gaba daya, hakan yasa na hakura na koma Abuja don cigqba da kallon yadda zaben zai kasance duk da cewa ban samu damar yin zaben ba saboda matsalar Card Reader ….
Read Also:
Kasar ta dauki dumi an cigaba da yada labarun karya wadanda zasu iya haifar da rigingimum da zasu iya tarwatsa ya, wanda hakan yasa cikin gaggawa naga akwai bukatar nayi wani abu cikin gaggawa wanda zai samar da zamam lafiya, tun kafin a gama kirga kuri’u sai naga jihar Lagos sun fara shagulgulan murna, yankin arewa ma rahoton sirri ya riskeni akan suna ta murna kuma suna shirin tayar da rigima duk a lokaci daya, ga daya daga cikin wakilai na a wajen tattara kuri’u ya kasa hakuri har yayi jayayya da shugaban hukumar zabe Jega a lokacin duk da cewa akan gaskiya yake, amma tunda an riga a yada labarun karya sai ake ganin kamar ko wani abu ake shirinyi na rashin gaskiya, kusan komai ya rikice a kasar komai zai iya faruwa, hakan yasa cikin kankanin lokaci na yanke shawarar yin abun dazai dorar da zaman lafiya a kasar, duk da nasan baa kayar dani a zabe ba amma na yanke shawarar da itace ta samar da wannan yanayin da al’umma suka tsinci kansu, duk da sunyi zaton kamar hakan ne zai zama jin dadi a tare dasu….
Ina da masaniya akan magudin zabe da aka tabbatar jam’iyyar APC tayi a yankuna masu yawa a kasar, ina sane da cin zarafin da akewa yan jam’iyyarmu ta PDP a gurare masu yawa, hatta cin amanar da wasu makusantanmu sukayi mana duk na samu labari, amma sai bangaren zaman lafiya dake zuciyata ya rinjayeni har na yanke shawarar zanyi abun danayi duk da cewa dukkan mutanen dake tare dani basu da masaniya akan wannan hukuncin dana yanke, don nasan bazasu taba barina nayi ba, amma ni bani da burin wani ya rasa ransa saboda ina son kasancewa akan mulki…..
Hukunci ne maigirma na dauka a wannan lokacin, sadaukarwa ce nayi wacce shugabannin aftica basa iyayi, na tabbata mai karatu zai yarda dani akan cewa ba karamar sadaukarwa nayi ba, nayi haka ne kawai saboda samar da cikekken zaman lafiya a kasar….
Falo na a cike yake da ministoci, masu bani shawara tare da masu temakun muna kallon yadda kawo sakamakon zabe ke tafiya, dukkan shugabannin tsaro na kasar suna tare dani a falon, shi kansa babban Alkalin alkalai na kasar yana zaune a falon, nasan cewa basu bari inyi abun dana yanke shawarar yi ba a lokacin hakan yasa na tashi na shiga cikin daki kamar zan shiga Toilet ne, amma basu san cewa zuwa nayi na dauki waya ba, inda na danna lambobin wayar Muhammadu Buhari bayan dan karamin jinkiri sai lambar tawa ta shiga cikin wayarsa inda aka daga a daya bangaren sannan akace….
Buhari: “Hello Your Excellency!”
Me: Your Excellency, how are you?”
Buhari: “I am alright, Your Excellency”
Me: “Congratulations!”
Buhari: “Thank you very much Your Excellency
Wannan kiran wayar danayi shine ya samar da cikekken zaman lafiya tare da kwanciyar hankali a lokacin, duk da cewa nasan ban fadi zabe ba amma nayi hakan saboda bawa siyasar kasarmu sabon yanayin da baa taba yiba a cikinta…..
Wani sashi kenan daga cikin littafin Jonathan wanda ya kaddamar a jiya…..
Daga Muzammil Mandawari
The post Yanayin da na kasance lokacin fadar sakamakon zaben 2015 – Goodluck Jonathan appeared first on Daily Nigerian Hausa.