Majalisar dokokin jihar Sakkwato a ranar Alhamis zata tantance Alhaji Munir Dan Iya domin zama sabon mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato tun bayan murabus din da tsohon mataimakin Gwamnan yayi.

Dan Iya dai ada shi ne dan takarar jam’iyyar PDP na Gwamnan jihar Sakkwato a lokacin da Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ke neman takarar Shugaban kasa a PDP.

Bayan Gwamnan ya gaza samun takarar Shugaban kasa ne, PDP ta baiwa Tambuwal damar tsayawa takarar Gwamnan jihar karo na biyu. Inda ta janye sunan Mannir Dan Iya ta maye gurbinsa da Aminu Waziri Tambuwal, inda shi kuma aka saka masa da kujerar mataimakin Gwamna.

The post Majalisar dokokin jihar Sakkwato zata tantance Mannir DanIya dan zama mataimakin Gwamna appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here