Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya bayyana cewar akalla mutum goma ne suka rigamu gidan gaskiya a rikicin manoma da makiyaya da ya kaure a yankin karamar hukumar Safana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da wata kungiyar fafutikar kare mata da kananan Yara ta kai masa ziyara a fadarsa a ranar Laraba.

“Mun samu rahoto a ranar Lahadi wasu bakin Fulani sun yiwa karamar hukumar Safana tsinke, inda suka farwa gonakin mutane suka cinye su sannan suka kashe mutum goma a cikin manoma”

“Sarkin ya Kara da cewar wannan abinda ya faru sharrin kwaya ne, yadda za a ce Yaro kankani ya kashe mace sa’ar mahaifiyarsa kuma ya yiwa gawar fyade “ Idan ba kwaya ba ba abinda zai sanya mutum haka.

The post Mutum 10 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a jihar Katsina appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here