‘Yan Banga Sun Dakatar da Niyyar Masu Garkuwa da Mutane a Abuja
Yan banga sun fattaki masu garkuwa da mutane a garin Kekeshi a Abuja
Yan bindigan sunyi niyyar afkawa garin ne a daren ranar Juma’a amma ba su yi nasara ba
Ɗaya daga cikin yan bangan da ya fita fitsari ne ya ankarar da yan uwansa suka fattaki yan bindigan
Yan banga sun dakile harin da wasu da ake zargi masu garkuwa ne suka kai a garin Kekeshi a ƙaramar hukumar Abaji a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
An sace mutum hudu a garin ciki har da wani yaro mai shekaru 14 kuma har yanzu ba a sako su ba, masu garkuwar na neman Naira miliyan 10.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakayya sunansa ya ce lamarin ya faru a ranar Juma’a da ta gabata da dare misalin ƙarfe 9.22 na dare.
Read Also:
An ruwaito cewa wasu da ake zargi masu garkuwa ne sunyi yunkurin sace wasu mutane a gidajen da ke wajen garin.
Ya ce wani ɗan banga a garin ya tafi yin fitsari ne sai ya hangi hasken fitila daga nesa.
“Daya daga cikin yan banga da ke zaune a nan ya tafi fitsari a bayan gida sai ya hango hasken fitila, shima sai ya haska fitilar sa,” in ji shi.
Ya ce daya daga cikin masu garkuwar ya harbi bindiga a iska bayan ganin hasken fitilarsa hakan yasa sauran yan bangan suka fara harba nasu bindigan.
Ya ce harbin da yan bangan suka yi ne yasa masu garkuwar suka tsere.
“Yan bangan sun yi musayar wuta da su har zuwa wani kududufi a wajen garin har sai da suka tsere,” in ji shi.
Kakakin yan sandan birnin tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf bata amsa sakon text ɗin da aka aike mata ba game da afkuwar lamarin.