Kano: ‘Yan Bautar Kasa Sun Gamu da Fushin Sojojin da ke Koya Musu Fareti

 

‘Yan bautar kasa sun gamu da fushin sojojin da ke koya musu fareti a sansanin bautar kasa ta jahar Kano.

An gano wani bidiyo lokacin da wasu ‘yan bautar kasa a Kano ke shanye a rana bisa laifin kin halartar filin fareti.

Mutane da dama a kafar Instagram sun yi martani, inda kowa ya bayyana ra’ayinsa kan wannan lamari.

Kano – Mutane da dama sun martani biyo bayan ganin wani bidiyo na membobin bautar kasa na NYSC da aka tilastawa bacci cikin zafin rana.

Legit.ng ta tattaro cewa an yi wa yan bautar kasa da ke zama a sansanin NYSC ta jahar Kano wannan hukuncin ne bisa laifin kin halartar filin fareti.

A cikin bidiyon da Instablog9ja ya yada a kafar Instagram, ya nuna lokacin da wasu ‘yan NYSC ke bacci a tsakar rana, wasu kuwa sun dauki abin wasu suna ci gaba da annushuwarsu.

‘Yan bautar kasa sun kwanta a rana a kan katifunsu, alamu sun nuna an hukunta ‘yan bautar kasan ne.

Martanin jama’a a kafar Instagram @koko_son_of_a_gun ya yi martani da cewa:

“Lmfaooooooooo. Na yi zaman sansani a Kano na shirin NYSC. Daga karaye junction zuwa sansanin da kanta babu wanda ya iya turanci sai mutum daya da ya sayar min bokiti. Direban da ya kaini garin Kano bai iya magana da turanci ba shi ma.”

@sandie_bgfl ya ce:

“Wannan mutumin da ya kwanta sakaka tare da shimfida kafafunsa ya bani dariya.”

@daisyijay ya ce:

“Omo, kwanakin nan ina karkashin gado nake buya, babu yadda sojojin za su gan ni”

@timz_0 yayi sharhi:

“Idan na dauko mayafi na lullube jikina ko,,, zance ya kare ,,, su da kansu za su zo su ce na tashi.”

@keshacosmetics opined:

“A nan ne na yi zaman sansanin bautar kasa, wahalar ba daga nan take ba, daga harbe-harbe, zuwa tsananin zafi, da safiya mai tsananin sanyi da tsoron macizai”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here