‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Wasu  Mutane Jahar Katsina

Yan bindiga sun sake kai hari garin Albasun Liman Sharehu da ke karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina.

A harin da suka kai na biyu, yan bindigan sun sake yin awon gaba da mutane guda tara don maye gurbin 8 da suka tsere.

Mutanen da aka yi garkuwar da su sun samu nasarar tserewa ne a yayin da ‘yan bindigan da suka sace su ke sharbar barci .

Wasu ‘yan bindiga, cikin fushi, sun sake kai hari garin Albasun Liman Sharehu dake yankin karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina tare da yin garkuwa da mutane tara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun sake kai harin kauyen ne da sanyin safiyar ranar Laraba.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa daga cikin mutanen da ‘yan bindigar suka yi garkuwar da su akwai wani dalibin aji biyar a babbar sakandire ta Damari, wanda aka sace tare da mahaifinsa.

Kafin wannan harin, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen a ranar Kirsimeti tare da yin garkuwa da mutane takwas cikinsu har da matan aure biyu.

Sai dai, dukkan mutanen takwas da aka sace tare da yin garkuwa da su a makon da ya gabata sun samu damar tserewa yayin da ‘yan bindigar ke bacci.

A cewar wata majiya da ke kauyen, ‘yan bindigar sun fusata ne shine suka sake dawowa sakamakon tserewar mutanen tare da kama wasu a matsayin madadinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here