Yan Bindiga Sun Harbe ‘Dan Takarar Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Kachia na Jahar Kaduna

 

Miyagun ‘yan bindiga sun sheke Alamkah Dominic Usman, dan takarar shugabancin karamar hukuma na APC a Kachia.

Dominic yana kan hanyarsa ta zuwa jahar Binuwai ganin iyalinsa yayin da miyagun suka tare shi tare da sheke shi.

Shine dan takara a karkashin inuwar jam’iyyar APC a zaben kananan hukumomi da za a yi ranar 14 ga watan Augusta .

Kachia, Kaduna – Dan takarar jam’iyyar All Progressive Chairmanship Congress (APC) na karamar hukumar Kachia na jahar Kaduna, Alamkah Dominic Usman wanda aka fi sani Cashman ya sheka lahira bayan wasu miyagun ‘yan bindiga sun harbe shi a jahar Benue.

A yayin zantawa da Daily Trust, shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Kachia, Alhaji Ahmed Tijjani Sulaiman, ya ce an harbe Usman a wani wuri a jahar Benue.

Usman yayi tafiya zuwa Binuwai, sai labarin mutuwarsa aka ji.

Alhaji Sulaiman ya ce, Usman amintaccen dan jam’iyya ne kuma ya hadu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jahar Binuwai inda iyalinsa ke zama, bai san cewa yana dab da amsa kiran ubangijinsa.

“Ba mu ji daga wurinsa ba tun bayan da ya bar Kachia daga jahar Binuwai a ranar Alhamis, sai kwatsam muka ji labarin cewa an kashe shi.”

Har zuwa mutuwarsa, shine dan takarar shugabancin karamar hukuma a Kachia dake jahar Kaduna.

Ana shirin za a yi zaben a ranar Asabar, 14 ga watan Augustan 2021.

Za a birne dan siyasan a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, Daily Trust ta wallafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here