‘Yan Bindiga Sun Harbi Kwamishinan Harkokin Kasuwanci na Jahar Imo
A wani rikici a jahar Imo, ‘yan bindiga sun bindige wani kwamishina tare da wasu mutane.
Bincike ya tabbatar da faruwar lamarin, in da afkawa motar wasu mutane da kuma kwamishinan.
Rundunar ‘yan sandan jahar ta ce tuni ta tattara wadanda lamarin ya rutsa dasu zuwa asibiti.
Wasu sabbin bayanai sun bayyana a ranar Litinin kan yadda wasu ‘yan bindiga suka harbi Kwamishinan Harkokin Kasuwanci na Jahar Imo, Iyke Ume.
An ruwaito cewa akwai fargaba a Owerri, babban birnin jahar, yayin da ‘yan bindiga suka harbe akalla masu motoci hudu a wani harin a daren Lahadi.
Lamarin ya faru ne a Orji, kan titin Owerri- Okigwe kusa da hedikwatar ‘yan sanda reshen shiyya ta biyu.
Daya daga cikin direbobin da aka harba yana tuka motar jami’an tsaro mara lamba. Yana tuki a cikin motar, lokacin da suka keta shi sau biyu, suka harbe shi kafin su farma wasu motocin, gami da bas na kasuwanci.
Read Also:
Lamarin ya kawo karshen harkokin kasuwanci a yankin yayin da mutane, ciki har da wadanda ke shan giya a shagunan da ke kusa suka yi ta gudu don kare lafiyarsu.
Bincike da aka gudanar ya nuna cewa kwamishanan yana mota ne tare da Mashawarci na Musamman kan Harkokin Jam’iyya, Dominic Uzowuru, zuwa gidansa da ke Orji, lokacin da ’yan bindigan suka keta shi sau biyu suka harbe shi a kafa da hannu.
Binciken jaridar Punch ya kuma gano cewa an harbi kwamishinan ne lokacin da yake sauke Uzowuru a gidansa da ke Orji bayan ganawa da wani kwamishina.
Lokacin da aka tuntubi mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin jam’iyya, Dominic Uzowuru, ya tabbatar da cewa an harbi Kwamishinan.
Ya ce, “Ba a harbe ni ba. An harbi Kwamishina. An kwace wayata da na kwamishinoni. Muna dawowa ne daga hidimar wakar dan uwanmu, Austin Nnawuihe. Yana sauke ni ne lokacin da ‘yan bindigan suka afka mana. Ina lafiya da yardar ubangiji. ”
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda, Orlando Ikeokwu, ya ce ‘yan sanda sun kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin lafiya na tarayya dake Owerri.