Mayakan Boko Haram Sun Kusa Shiga Babban Birnin Kasar Nan – Gwamna Abubakar Sani Bello

 

Gwamnan jahar Neja ya bayyana cewa, ‘yan Boko Haram na daf da shiga birnin Abuja idan ba a kula ba.

Ya gargadi cewa, tsakanin in da suke yanzu a jahar Neja da Abuja tafiyar awanni biyu ne kacal.

Ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira in da ya tarar da mata da dama Gwamna Abubakar Sani Bello na ja
har Neja ya ce mayakan Boko Haram sun yi kusa da babban birnin kasar., Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana lokacin da ya ziyarci sansanin ‘Yan Gudun Hijira a ranar Litinin, gwamnan ya ce ‘yan ta’addan sun karbe wani yanki na jahar bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza a kokarin samar da tsaro a jahar.

Ya ce ya tuntubi Gwamnatin Tarayya a lokuta daban-daban amma babu wani abu mai amfani da ya fito daga kokarinsa.

Bello ya yi gargadin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na kokarin mai da Kaure a karamar hukumar Shirroro da ke jahar ta zama hedikwatarsu kamar yadda suka yi a dajin Sambisa a jahar Borno.

Saboda da haka, ya ce yayin dajin Sambisa ke da nisan kilomita da yawa daga Abuja, tsakanin Kaure da Abuja awanni biyu kawai.

“Na nemi taimakon gwamnatin tarayya amma abin takaici lamarin ya kai ga wannan matakin kuma idan ba a kula ba, hatta Abuja ba za ta tsira ba. Mun dade muna fadin haka amma duk kokarin da ake yi ya zama a banza.”

Da yake jawabi kan yawan ‘yan gudun hijirar da ke sansanin, Bello ya ce wasu daga cikinsu sun fara komawa gida yana mai cewa mafi yawansu za su ci gaba da zama a sansanin saboda ‘yan ta’adda sun kwace garuruwansu da kauyukansu.

A lokacin ziyarar gwamnan, akwai yara 1,447, mata masu ciki 119 da wasu mata 447 a sansanin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here