Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai a Nigeria, NBC ta Dakatar da Gidan talabijin na Channels Television

 

Hukumar NBC ta dakatar da gidan talabijin na Channels Television tare cinta tarar Naira miliyan 5.

NBC ta ce Channels Television ta yi hira da shugaban IPOB inda ta bari yana ta furta kalaman da suka saba dokoki aiki

Hukumar da ke kula da kafafen watsa labarai a Nigeria, NBC, dakatar da gidan talabijin na Channels Television daga watsa shirye-shirye saboda saɓa dokokinta.

Kazalika, an kuma ci gidan talabijin cin tarar Naira miliyan 5.

A cikin wasikar da NBC ta aika wa shugaban Channels Television mai ɗauke da sa hannun shugabanta Armstrong Idachaba, hukumar ta ce an dauki matakan ne saboda shirin kai tsaye da ta watsa misalin ƙarfe 7 na yamma ranar Lahadi 25 ga watan Afrilun 2021.

A cewar NBC, gidan talabijin ɗin ta saba doka saboda bawa shugaban kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biafra, IPOB, ta furta kalamun ɓallewa daga ƙasa da tada rikici ba tare da yi masa gyara ko gargaɗi ba.

Mista Armstrong ya ƙara da cewa hakan ya saba wa dokokin watsa labarai. Ta kuma zargin gidan talabijin ɗin da barin baƙonta ya furta kalaman cin mutunci, ƙarya kan Rundunar sojojin Nigeria duk da cewa kotu ta haramta kungiyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here