‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Jahar Zamfara
Wasu ‘yan bindiga dadi sun kai hari garin Magarya, karamar hukumar Zurmi, jahar Zamfara.
‘Yan bindigar sun kashe mutane uku, sun sace shanu fiye da 100 tare da kone rumbunan da jama’a suka adana kayan abinci.
Garin Magarya ne mahaifar Alhaji Nasiru Muazu Magarya, shugaban majalisar dokokin jahar Zamfara.
Wasu ‘yan bindiga dadi sun kai garin Magarya da ke yankin karamar hukumar Zurmi, jihar Zamfara, a ranar Talata.
Garin Magarya ne mahaifar shugaban majalisar dokokin jahar Zamfara, Alhaji Nasiru Muazu Magarya.
Read Also:
“Wasu ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai sun dira garin Magarya tare da budewa jama’a wuta.
“Sun hallaka mutane biyu nan take, sun lalata dumbin dukiya tare da yin awon gaba da shanu fiye da 100 bayan sun kone rumbunan da jama’a suka adana abinci,” kamar yadda wani dan majalisa ya shaidawa Daily Trust.
A ranar Laraba ne Honarabul Muazu ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati zuwa garin Magarya domin jajantawa jama’a akan abinda ya faru.
Dagacin Magarya ya zagaya da tawagar jami’an domin su ganewa idanuwansu irin barnar da ‘yan bindiga suka tafka a garin.
A yayin da yake gabatar da jawabin jaje, Honarabul Muazu ya dauki alkawarin za’a turo karin jami’an tsaro zuwa yankin domin zakulo ‘yan ta’adda.