‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Jihar Taraba Sun yi Garkuwa da ‘Dan Kasuwa

 

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari masallacin Jalo Junction, Jalingo, Taraba.

Maharan sun afka masallacin ne a yammacin ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba a lokacin da al’umma ke sallar Magariba.

Masu garkuwan sun halaka masallaci guda daya sun kuma yi awon gaba da wani dan kasuwa da dansa dan makarantar sakandare.

Taraba – Wasu masu garkuwa da mutane kimanin su 10 sun kai hari wani masallaci a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba a ranar Alhamis.

Maharan sun kashe mutum daya sun kuma sace wani dan kasuwa da dansa, Daily Trust ta rahoto.

Masu garkuwan sun afka masallacin da ke Jalo Junction ne a unguwar Saminaka na Jalingo da yamma yayin sallar Magariba.

An ce dan dan kasuwan dalibi ne a makarantar sakandare.

Maharan sun tilasta wa mutane da dama yin hijira

Rahotanni sun ce masu garkuwan sun kashe mutane da dama, ciki har da dan sanda tare da sace fiye da mutane 30 a cikin yan watanni.

Masu garkuwa da ke kai hare-hare a tsaunikan har zuwa rafin Lamurde a karamar hukumar Ardo_Kola sun tilasta wa mutane da dama barin gidajensu.

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, amma ba a iya samunsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here