Jami’an Hukumar Mozambique Sun Kwace Wayoyin Iphone na Jabu Kimanin 1,165

 

Hukumomin kasar Mozambique sun ce sun kwace wayoyin iphone na jabu kimanin 1,165, tare da kama wasu mutum biyu ‘yan China bisa zargin gudanar da masana’antar, wadda ke Maputo babban birnin kasar.

‘Yan sanda sun ce ana zargin masu masana’antar da kera wayoyin iphone na jabu.

Wadanda ake zargin dai sun musanta aikata ba daidai ba.

Jami’an hukumar hana fasa kwauri ta kasar ta ce ta samu nasarar kama mutanen bayan da suka samu bayanan sirri.

Babban daraktan hukumar mai kula da birnin Maputo Gino Jone, ya ce hukumarsa ta samu korafi game da zargin, inda suka kaddamar da bincike ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce ”bayan binciken da muka gudananr na tsawon mako uku, sai muka gano masana’antar”.

Ya kara da cewa ”Wani gini ne da ake gudanar da masana’antar, ana kera wayoyin tare kuma da sayar da su a wani shago da ke yankin Alto-Maè.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here