Karyewar Gada a Indiya ta yi Sanadiyyar Kashe Mutane 141

 

Masu aikin ceto na ci gaba da lalubo gawarwakin mutanen da suka nutse a kogi, sakamakon karyewar gada a gundumar Morbi da ke jihar Gujarata,

Akalla mutum 141 ne suka mutu a karyewar tsohuwar gadar wadda aka gina tun zamanin mulkin mallaka.

Akwai akalla jami’ai 500 daga hukumar kiyaye hadura da aukuwar bala’i ta kasar domin aikin ceton.

Haka kuma jami’an sojin kasar na taimakawa wajen gudanar da aikin.

Jami’an na amfani da kananan jiragen ruwa domin lalubo gawarwakin wadanda suka nutsen.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here