Jami’an Tsaro Sun Kama Masu Safarar ‘Yan Mata 3 Sun Ceto Mata 50

 

 

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta samu nasarar kubutar da ‘yan mata 50, wadanda ta yi zargin cewa an tilasta musu shiga karuwanci a wasu gidajen karuwai biyu a birnin Fatakwal da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Jaridar The Cable a Najeriya ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na sansanin sojin ruwa da ke jihar Richard Iginla, na bayyana cewa a yayin samamen sun kama mutum uku da suke zargi da safarar ‘yan matan -wadanda wasunsu shekarunsu ba su fi 14 ba – domin tilasta musu yin karuwanci.

Ya ce Sun kaddamar da samamen ne tare da hadin gwiwwar hukumar yaki da safarar bil-adama ta kasar wato (NAPTIP) da kuma rundunar tsaro da Civil Defence.

Ya ci gaba da cewa ”Mun samu bayanan sirri daga hukumar NAPTIP, wadda ta dade tana bibiyar gidajen karuwan da ake tilasta wa mata galibinsu ‘yan mata yin karuwanci. Daga nan sai muka shirya rundunar hadin gwiwwa cikin gaggawa muka kuma samu nasarar kubutar da wadannan mata’.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here