Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda a Katsina, Sun Kashe Jami’i

 

Yan bindiga sun kashe ɗan sanda ɗaya yayin da suka kai hari caji ofis a wani ƙauyen karamar hukumar Batsari a Katsina.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun yaudari jami’an yan sandan ta hanyar sanya Hijabi, sun far musu aka yi musayar wuta.

Kakakin ƴan sanda ya bayyana cewa an samu nasarar dakile harin amma sun kashe mutum ɗaya, sun jikkata wani.

Jihar Katsina – Wani jami’in rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ya rasa rayuwarsa yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari wurin da yake aiki a Batsari.

Jaridar Punch ta tattaro cewa ƴan bindigan sun sanya Hijabi sun ɓoye fuskokinsu yayin da suka farmaki caji ofis a kauyen Saki Jiki da ke ƙaramar hukumar Batsari a Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ranar Jumu’a, 19 ga watan Janairu.

Ya ƙara da cewa baya da kashe ɗan sanda ɗaya, maharan sun kuma jikkata wani jami’i guda ɗaya a harin.

Yan sanda sun yi nasarar dakile harin Ya ce lamarin ya faru ne da karfe 8 na daren ranar Alhamis, inda ya kara da cewa tuni ‘yan sanda suka ɗauki mataki kan lamarin.

A sanarwan da ya fitar, mai magana da yawun ƴan sandan ya ce:

“Jiya (Alhamis) da misalin karfe 8:00 na dare wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi suka kai hari a ofishin ƴan sanda dake kauyen Saki Jiki a karamar hukumar Batsari.

“Jami’an ƴan sanda sun mayar da martani cikin jarumtaka kuma sun yi nasarar dakile harin. Sai dai jami’i daya ya rasa ransa sannan wani ya samu rauni sakamakon harin.

“Zamu fitar da karin bayani idan bukatar hakan ta taso kan wannan hari nan gaba.”

A baya-bayan nan ‘yan bindiga sun ƙara matsa kaimi wajen kai hare-hare a jihar Katsina, inda karamar hukumar Batsari kaɗai ta fuskanci hare-hare akalla biyu a mako.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com