Rundunar ‘Yan Sanda ta Kama Gawurtaccen Mai Garkuwa da Mutane a Kaduna

 

Rundunar ‘yan sandan Abuja babban birnin Najeriya ta tabbatar da kama Chinaza Phillip, wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna.

Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar ta wallafa a shafinta na X ta ce ‘yan sandan jihar Kaduna ne suka kama mai garkuwa da mutanen.

Sanarwar ta ce tuni aka miƙa shi hannun rundunar ‘yan sandan Abuja a ranar Juma’a, domin ci gaba da gudanar da bincike.

A ranar Alhamis 18 ga watan Janairu ne ‘yan sandan jihar suka kama ɗan fashin a daidai lokacin da shi da sauran abokan sana’arsa suke kan hanyar zuwa Kano daga Abuja, lokacin da suka yi garkuwa da wani mutum a Abujan, suka kuma tafi da shi a motarsa.

Rundunar ta ce ta kuma gano wasu makamai da wayar hannu da kuma motar mutumin da suka yi garkuwar da shi ɗin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com