‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaron Najeriya 12 a Jahar Zamfara

 

Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaron Najeriya 12 a wani hari da suka kai karshen makon da ya gabata kan wani sansanin sojoji a jahar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar, kana suka sace makamai da kona gine -gine, in ji majiyoyin tsaro.

Ba a dai bayyana ko su wanene suka kai samamen na ranar Asabar a Mutumji ba, amma sojoji na ci gaba da luguden wuta kan ‘yan fashin daji wadanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane.

An kuma katse hanyoyin sadarwa a Zamfara da wasu sassan makwabciyar jihar Katsina a kokarin hana yan fashin sakat.

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa “Maharan sun kutsa cikin sansanin ne da misalin karfe 10:30 na safe kuma suka fafata da sojojin a wani mummunan artabu,” in ji wata majiyar tsaro.

“Sun fatattaki sojojin sun kashe 12 daga cikinsu. da suka hadar da sojojin ruwa tara, da soja da ‘yan sanda biyu.”

Sansanin da ke Mutumji, gundumar Dansadau, mai tazarar kilomita 80 daga Gusau babban birnin jahar, muhimmin wuri ne da sojojin kasar ke amfani da shi wajen shirya dabaru da tattara bayanai a yakin da suke yi da yan bindiga a jahar.

Zuwa yanzu dai rundunar sojojin Najeriya bata ce komai dangane da batun ba tukunna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here