Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci a Jihar Kaduna, Sun Kashe Limami

Yan bindiga sun kai hari Masallaci lokacin sallar asuba a ƙauyen Sabon Layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun kashe limamin Masallacin tare da wani mutum ɗaya yayin da wasu masallata biyu suka ji raunuka.

Har yanzun babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Kaduna ko hukumar ‘yan sanda.

Jihar Kaduna – Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari Masallaci a ƙauyen Sabon Layi da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna lokacin Sallar Asuba yau Talata.

Ƴan ta’addan sun kashe limamin Masallacin da wani mutum ɗaya mai suna Kabiru, yayin da wasu ƙarin masallata biyu suka ji raunuka daban-daban.

Bilya Mairabo da Ashiru Mairabo, su ne suka ji raunuka yayin harin kuma yanzu haka suna kwance a babban Asibitin Jibrin Maigwari a Birnin Gwari ana musu magani.

Wani Basarake a yankin, Zubair AbduRrauf, ya shaida wa Punch ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5 na safe, Vanguard ta ruwaito.

Harin ‘yan bindiga ya zama ruwan dare a Birnin Gwari AbduRrauf, wanda ke rike da sarautar Danmasanin Birnin-Gwari, ya ce kusan kullum ‘yan bindiga sai sun kai hari a kauyukan Birnin-Gwari.

A cewarsa, suna kashe rayukan al’umma, su yi garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa, musamman ma manoma.

Ya kara da cewa lamarin ya fi muni a babban titin Birnin-Gwari zuwa Kaduna, wanda a yanzu ya zama ruwan dare ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.

A kalamansa ya ce:

“Eh, an kashe limamin masallaci da wasu masallata biyu. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar ranar Talata.Wasu masallata biyu suna babban asibitin Jibrin Mai Gwari, Birnin-Gwari ana musu magani.”

“Muna cikin wani mawuyacin hali a Birnin-Gwari. Ko a kan babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, mutane ba su iya wucewa sai da rakiyar jami’an tsaro ko ‘yan banga.”

“Kwanaki biyu da suka gabata ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu da suke dawowa daga Kaduna. Suna kawo hari kusan kowace rana. Jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu amma akwai bukatar canja dabaru.”

Hukumomi sun san abin da ya faru?

Kawo yanzu dai babu wani sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Kaduna ko kuma rundunar ‘yan sandan har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya bayyana cewa yana wani abu ne, ba zai iya magana ba a yanzu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com