An ci Tarar Kano Pillars Naira Miliyan ɗaya

A ranar Litinin ne aka ci tarar Kano Pillars kuɗi har Naira miliyan ɗaya, sakamakon kutsen da magoya bayanta suka yi a filin wasa, lokacin da suka fafata da Rivers United.

An tabbatar da cewa magoya bayan ƙungiyar Kano Pillars sun ketara shingen filin wasa domin murnar cin ƙwallon da suka yi a minti na 92 ​​a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha.

Bayan nazarin rahotanni daga jami’an wasan, hukumar kula da gasar Firimiya ta Najeriya, NPFL ta tuhumi kulob din da laifin karya doka mai lamba B13.18.

Don haka an umurci kulob din da ya biya tarar cikin kwana 14 kuma ya ja kunne kan hakan, wanda gaza yin hakan zai zamo tamkar ci gaba da saɓa wa dokokin hukumar ta NPFL.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com