‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Sojoji 4 a Jihar Katsina
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta a harin da ‘yanbindiga suka kai wa sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Tun da farko rahotonni sun ce maharan sun auka wa sansanin rundunar Operation Hadarin Daji ne a ranar Lahadi, inda suka kashe sojoji biyar tare da raunata wasu 11.
Read Also:
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust kisan amma ya ce huɗu ne, ba biyar ba kamar yadda aka ruwaito tun da farko.
“A ranar 12 ga watan Mayu, dakarun Hadarin Daji suka gamu da kwanton ɓauna biyu a ƙauyen Kuran Mota da kuma kusa da Alikere da ke ƙauyen Yarmalimai na jihar Zamfara,” in ji shi kamar yadda jaridar ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa “duk da cewa dakarun sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen kare kansu, abin baƙin ciki an kashe sojoji huɗu daga cikinsu kuma aka jikkata uku a harin farko”.
A hari na biyu kuma, sojoji biyar ne suka jikkata sakamakon harbin bindiga, kuma an ba su kulawar da ta dace bayan kai su garin Faskari, in ji shi.