Yan Bindigan da Suka yi Garkuwa da ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa Sun buƙaci Kuɗin Fansa
Yan bindiga sun turo saƙon kuɗin fansar da su ke buƙatar a biya gabanin su sako ɗaiban jami’ar jihar Nasarawa.
A ranar Litinin da daddare, masu garkuwan suka yi awon gaba da ɗalibai mata huɗu a gidajensu na wajen makaranta a Keffi.
Wata majiya ta ce a halin yanzu sun kira waya, sun nemi a haɗa musu Naira miliyan 80 jimulla.
Nasarawa – Miyagun ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da ɗalibai mata 4 na jami’ar jihar Nasarawa sun gindaya sharaɗin kuɗin fansar da su ke buƙata kafin su sako su.
Rahoton Leadership ya nuna cewa waɗanda suka yi garkuwa da ɗaiban sun buƙaci a haɗa musu Naira miliyan 80 a matsayin kuɗin fansa.
Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda maharan suka yi awon gaba da ɗalibai huɗu a Angwan Ka’are da ke ƙaramar hukumar Keffi, ranar Litinin da ddadare.
Read Also:
Daliban da aka sace sun hada da Rahila Hanya (SLT), Josephine Gershon (Kimiyyar Kwamfuta), Rosemary Samuel (Kasuwanci), da Goodness Samuel (Geography).
‘Yan bindigan sun kai farmaki gidan ɗaliban da ke wajen makaranta da misalin ƙarfe 10:30 na dare, kuma suka yi awon gaba da su.
Yan bindiga sun tutuɓi makusantan ɗaliban
Sai dai a halin da ake ciki, wata majiya ta shaida wa jaridar cewa ‘yan bindiga sun kira ɗaya daga cikin masu alaƙa da lamarin, inda suka faɗi buƙatarsu gabanin su saki ɗaliban da suka sace.
A ruwayar Dailypost, majiyar ta ce:
“Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi wadanda suka dace kuma sun bukaci a biya su Naira miliyan 80 domin su sako daliban.”
“Jimullar kuɗin fansar ɗaliban guda huɗu shi ne Naira miliyan 80, ma’ana suna neman Naira miliyan 20 kan kowace ɗaliba ɗaya.”
Ta ce duk da har kawo yanzun ba a cimma matsayar ƙuɗin da za a biya masu garkuwan ba, ana ci gaba da koƙarin ganin an ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.
Ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar ɗaliban jami’ar Nasarawa, Sanata Julius James K, wanda ya tabbatar da haka, ya ce sun maida hankali wajen ceto ‘yan uwansu.