‘Yan Bindigan da Suka Sace Mata da Yaranta 2 a Abuja Sun Nemi Kudin Fansa
Barayin da suka jagoranci sace matar wani babban malamin addinin kirista a Abuja da ƴaƴansa mata biyu sun nemi fansa.
Wata majiya tace maharan sun kira ɗaya daga cikin makusantan waɗanda aka sace ranar Lahadi da karfe 11:00 na dare.
Da farko ɓarayin sun nemi a biya miliyan N100m kuɗin fansa, amma daga bisani suk sakko zuwa miliyan N50m.
Abuja – Yan bindigan da suka sace iyalan Fasto a Abuja, matarsa da ƴaƴansa mata biyu sun nemi a tattaro musu miliyan N50m kuɗin fansa.
Dailytrust ta rawaito cewa maharan sun farmaki gidan babban malamin dake Zone A, yankin Pegi, karamar hukumar Kuje, ranar Lahadi.
Yayin harin ne ɓarayin suka yi awon gaba da matarsa da yayan sa mata guda biyu, Glory Oladapo da Moyo Oladapo.
Read Also:
Rahotanni sun bayyana cewa Fasto Oladapo, wanda malamin cocin RCCG ne dake Pegi, ya yi tafiya zuwa wani gari lokacin da lamarin ya faru.
Yaushe ɓarayin suka kira iyalan malamin?
Wata majiya cikin iyalan faston, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace maharan sun gabatar da bukatarsu ranar Lahadi da daddare.
Yace ɓarayin sun kira ɗaya daga cikin iyalan waɗanda suka sace, inda suka bukaci a haɗa musu miliyan N100 kuɗin fansa da farko.
Yace:
“Sun kira waya ranar Lahadi da daddare da misalin karfe 11:00 kuma wanda suka kira ya yi magana da matar faston da yaran biyu.”
“Da farko ɓarayin sun nemi tsabar kuɗi miliyan N100m amma daga baya suka sakko zuwa miliyan N50m.”
Mutumin ya kara da cewa a halin yanzun an cigaba da tattaunawa da ɓarayin domin su rage makudan kuɗin da suka sanya.
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan Abuja, ASP Daniel Y Ndiparya, ya ci tura kuma bai daga kiran waya ba.