Sabon Hari: An Kashe Mutane 3 a Jahar Plateau

 

An halaka mutane uku a ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Bassa ta jahar Plateau a sabbin hare-haren da aka kai kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta rawaito cewa an kai hare-haren biyu ne mabanbanta a ƙauyuka biyu.

Harin na farko ya faru ne a ranar Lahadi da yamma a garin Kwachudu inda aka kashe wani makiyayi.

Shugaban kungiyar Makiyaya na Miyetti Allah, MACBAN, na jahar, Malam Nura Abdullahi ya zargi yan kabilar Irigwe da datse kan wani Musa Sale yayin da suka raunata Abdulsalam Nuhu yayin da suke kiwon dabbobi a Kwachudu.

Yan kabilar Irigwe sun musanta zargin, suna mai cewa ba gaskiya bane kuma babu wani hujja da ke nuna su suka aikata kisar.

Awanni bayan garin na yammacin Lahadi, an kashe yan kabilar Irigwe biyu a safiyar ranar Litinin a garin Renwienku a ƙaramar hukumar Bassa.

Malison David, ƙalla kungiyar yan Irigwe, IDA, ya zargi Fulani da kai harin amma kungiyar Fulani sun musunta zargin.

Harin na zuwa ne kwanaki biyar bayan kabilun biyu sun yi taron zaman lafiya da gwamnan jahar Simon Lalong sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Kakakin yan sanda na jahar, ASP Ubah Gabriel bai ɗaga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

Ku saurari ƙarin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here