‘Yan Bindigan da Suka Sace Mutane 5 ‘Yan Gida Daya a Jahar Kaduna Sun Nemi Kudin Fansa

 

‘Yan bindigar da suka sace mutane biyar ‘yan gida daya a unguwar Sauri da ke karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna sun tuntubi yan uwansu.

Maharan sun nemi a biya kudin fansa naira miliyan 20 kafin su sake su.

Yan bindigar dai sun yi garkuwa da magidanci mai suna Peter Andrew Umoh, matarsa da kuma ‘ya’yansa guda uku.

Masu garkuwa da mutanen da suka sace mutane biyar ‘yan gida daya a unguwar Sauri da ke karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna sun bukaci a biya naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, jaridar Aminiya ta rawaito.

An rahoto cewa maharan sun kai farmaki yankin ne inda suka yi awon gaba da wani mutum mai suna Peter Andrew Umoh, matarsa da kuma ‘ya’yansa guda uku.

Jaridar Daily Post ta kuma rawaito cewa tsufa ya tilastawa ‘yan bindigar kyale mahaifin mutumin mai shekaru 86 a duniya.

Sai dai kuma tsohon ya bayyana cewa a kaf danginsa gaba daya babu wanda yake da Naira miliyan 20 da maharan suka bukaci a biya.

ya ce:

“Ina rokon ’yan Najeriya da su taimaka min a ceto ’ya’yana da jikoki.”

Kanwar mutumin da aka yi garkuwa da shi, Misis Josephine Andrew, ta bayyana cewa ’yan bindigar sun ki karbar tayin N300,000 da iyalan suka yi musu.

Ta bayyana suna cikin halin fargabar kada ’yan bindigar su hallaka musu ’yan uwa, don haka tana neman taimakon ’yan Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here