‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’ar ABSU ta Jahar Abia
Wasu ‘yan bindiga sun sace daliban jami’ar ABSU ta jahar Abia a hanyar zuwa makarantar.
Rahoto a bayyana cewa, an sace daliban 10 tare da wasu mutane da ba a san adadinsu ba.
Wata majiyar tsaro ta ce, an samu motoci uku a wurin da aka sace daliban, lamarin yake nuni da cewa akwai wasu daban da aka sace.
Abia – Wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai 10 na Jami’ar Jahar Abia, Uturu (ABSU) a hanyar Ihube zuwa ABSU, Daily Sun ta rawaito.
Read Also:
Sace daliban na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da malaman jami’ar uku a kan hanyar Uturu/Isuikwuato.
Lamarin wanda rahotanni suka ce ya faru tsakanin karfe 5 na yamma zuwa 6 na yamma a ranar Asabar, ya jefa al’ummar jami’ar cikin rudani.
An ba da rahoton cewa motar bas ta jahar Abia da ke jigilar fasinjoji zuwa makarantar, SUV da mota kirar Hilux mallakar wani kamfani an same su babu kowa a ciki a wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuni da cewa ba daliban kadai aka sace ba.
Wata majiyar tsaro ta ce kawo yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.