‘Yan Bindiga Sun Saki Fursunoni 240 a Jahar Kogi

 

Jami’ai a jahar Kogi da ke Najeriya sun ce fursunoni dari biyu da arba’in sun tsere bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani gidan yari da ke karamar hukumar
Kabba/Bunu da yammacin ranar Lahadi.

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta ce maharan na dauke da muggan makamai.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba na cewa an kashe jami’an tsaro biyu.

Bayanai sun ce da isar ‘yan bindigar ne suka fara yin gumurzu da masu gadin gidan yarin, inda suka kutsa kai bayan sun cim musu.

Har yanzu dai mahukunta a kasar basu bayar da cikakken bayani dangane da yawan wadanda suka mutu ko suka jikkata sakamakon artabun ba.

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriyar ta ce fursunoni 294 ne ke cikin gidan yarin lokacin da aka kai harin, 240 daga cikinsu na jiran shari’a, yayin da kuma aka yanke wa 70 daga cikinsu hukunci.

Tuni babban kwanturolar hukumar Halliru Nababa ya umarci a kamo fursunonin da suka arce

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here