‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Kungiyar IPOB 2 Ya yin da 3 Suka Rasa Ransu a Jahar Imo

 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, ta kai wani samame a jahar Imo kan wata daba da ake zargin ta ‘yan kungiyar a-ware ta IPOB da bangaren tsaro na kungiyar ce, inda suka kama mutum 2, kuma wasu 3 suka rasa rayukansu.

Hakan ya auku ne yayin da jama’a suka fara bayyana gamsuwa da yadda kwanciyar hankali da walwala suka fara komawa jahar ta Imo da sassan yankin kudu maso gabashin Najeriyar.

Amma kuma ana ta kokawa game da umarnin da haramtacciyar kungiyar ta IPOB ta bayar a duk fadin yankin, cewa kowa ya zauna gida a duk ranakun Litinin, har sai an sako ja-goranta, Nnamdi Kanu, wanda hukumomin kasar ke tsare da shi bisa zarge-zargen da cin amanar kasa, da tayar da zaune tsaye.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here