Daliban Yauri: Yan bindiga Masu Garkuwa da Mutane Sun Sako Mutum 30
Bayan sama da kwanaki 120, wasu cikin daliban Yauri sun samu kubuta.
Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako mutum 30; dalibai 27, Malamai 3.
Yanzu saura sama da dalibai 60 hannun yan bindigan cikin daji.
Kebbi – Dalibai da Malaman makarantar sakandaren gwamnatin tarayya FGC, Birnin Yauri, jahar Kebbi, guda 27 da Malami uku sun samu kubuta daga hannun tsagerun yan bindigan da suka sace su.
Wadannan Dalibai da Malamai sun sha ne bayan sama da kwanaki 118 hannun yan bindiga.
DailyTrust ta rawaito cewa Gwamnan jahar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, ya bayyana hakan ga manema labarai.
Read Also:
Da yake sanar da hakan a ranar Alhamis, Gwamnan Atiku Bagudu, ya bayyana cewa daliban sun yi hakuri su dauki wannan matsayin jarrabawa.
A cewarsa:
“Annabawan Allah, wadanda su ne zababbun Allah, su ma Allah Ya jarrabe su; amma duk mutumin Allah Ya jarrabe shi ya yi hakuri tabbas ladarsa a wurin Allah ba ta da iyaka.”
Ya kara da cewa wadanda aka sako din sun hada da dalibai mata 2 da maza 25, sai malamai maza biyu da mace daya.
Gwamnan ya bayyana cewa sauran daliban dake hannun yan bindiga kuma ana cigaba da kokarin kubutar da su. Ya yi addu’an Allah ya taimaka wajen gano sauran.
Gwamnan ya kuma ba da umarnin a duba lafiyar daliban da malaman nasu da aka sako sannan a ba su tallafin da suke bukata kafin a mika su ga iyalansu.