Rikici ya Barke a Jahar Abia Bayan Sojoji Sun Harbe ‘Yan IPOB 5

 

Rikici ya barke a wani yankin jahar Abia yayin da wasu ‘yan IPOB suka fito yawon gangami.

Duk da cewa rahotanni ne da ba a tabbatar dasu ba, amma an ce sojoji sun harbe ‘yan IPOB biyar.

An ce sun fito ne da suka ji labarin an kawo shugaban kungiyarsu ta IPOB kotu a babban birnin tarayya.

Abia – Jaridar Daily Sun ta rahoto cewa, an samu tashin hankali a Arochukwu ta jahar Abia a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba yayin da jami’an tsaro ke fafatawa da ‘yan kungiyar awaren IPOB a yankin.

Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa mutane hudu da ake zargi ‘yan kungiyar IPOB ne ana fargabar an kashe su a yayin fafatawar

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here