‘Yan Bindiga Sun Aika da Wasikar Barazana ga Mutanen Kananan Hukumomin Sokoto
Miyagun yan bindiga sun aike da wasikar barazana ga mutanen ƙauyuka biyar a kananan hukumomin Sokoto.
Lamarin ya jefa mutanen yankunan cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar kan yaushe maharan zasu shigo.
Wasikar ta bayyana cewa babu wani karfin jami’an tsaro da zai hana su aiwatar da kudirinsu na kawo harin.
Sokoto – Yan bindigan da suka gudo daga jahar Zamfara, waɗanda suka kai hari kan kauyukan dake bakin boda a Sokoto makon da ya shuɗe, sun aike da wasikar cigaba da miyagun ayyukansu ga mutanen yankin.
Rahotanni sun nuna cewa harin yan bindigan a waɗannan yankuna ya hallaka mutane da dama yayin da suka fasa shaguna domin ɗibar kayan abinci.
Wace barazana yan bindigan suka yi?
Mutanen Kauyen Shuni sun shiga tashin hankali da zaman ɗar-ɗar, biyo bayan tsintar wasikar barazanar mahara da aka yi karkashin wata bishiya.
Read Also:
A cewar wani mazaunin kauyen, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, yace an tsinci wasikar ne a karkashin wata bishiya dake kauyen Kwanar Kimba, karkashin Shuni.
Mutumin yace:
“Takardar wasikar an rubuta ta da harshen Hausa, wanda ake zargin yan bindiga da barzanar tarwatsa kauyukan Shuni, Kwanar Kimba, Rikina da Dange, kuma hakan ya jefa al’umma cikin tashin hankali.”
A wasikar sun bayyana cewa babu wani karfin jami’an tsaro da zai hana su aiwatar da mummunan kudirinsu.
“Sojoji miliyan ɗaya ba su isa dakatar da mu kawo muku hare-hare ba, wanda zamu iya yi kowane lokaci daga yanzun.”
Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?
Har yanzun babu wani sako a hukumance da rundunar yan sanda reshen jahar Sokoto ta fitar game da lamarin, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.
Amma wata majiya da shaida wa yan jarida cewa har yanzun hedkwatar yan sandan jahar ba ta samu kwafin takardar daga DPO na yankin ba.