‘Yan Bindigar Jahar Adamawa Sun Tuba, Sun Miƙa Makaman su ga Rundunar ‘Yan Sandan Jahar
Wasu yan bindiga sun tuba da muggan ayyukansu, sun miƙa makaman su ga rundunar yan sanda a jahar Adamawa.
Kwamishinan yan sanda a jahar, Alhaji Aliyu, yace sun miƙa bindugu ƙirar G3 tare da alburusai.
Alhaji ya kira yi sauran yan bindigan dake jahar su gaggauta tuba su miƙa makaman su kafin jami’an yan sanda su iso garesu.
Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa, CP Aliyu Alhaji, a ranar Talata yace wasu yan bindiga biyu dake garkuwa da mutane sun miƙa makamansu ga hukumar yan sanda.
Da yake jawabi ga manema labarai a Yola, babban birnin jahar, Alhaji yace tubabbun yan bindigan sun miƙa bindigu ƙirar G3 guda biyu da kuma alburusai,.kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Read Also:
A cewar kwamishinan, har yanzun hukumar yan sanda na cigaba da bincike kan yanayin yadda mutanen suka mallaki bindigu.
Kuma ya tabbatar wa mutanen jahar Adamawa cewa yan sanda zasu tsare rayukansu da dukiyoyinsu, kamar yadda Pulse ta ruwaito.
Kwamishinan yayi kira ga sauran yan bindiga da su gaggauta tuba, su miƙa makaman su kafin yan sanda su kamo su.
Alhaji ya ƙara bayyana cewa daga watan Maris zuwa 25 ga watan Mayu jami’an yan sanda sun kama mutum 52 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
An kwato bindigu 20 da suka mallaka ba bisa ƙa’ida ba, alburusai 1000 da sauran makamai da suka kai na kimanin miliyan uku.
Yace:
“Daga Maris zuwa yau, jami’ai sun ƙaddamar da binciko maɓoyar yan ta’adda da masu gudanar da haramtattun ayyuka, inda a sakamakon haka suka ƙwato 50.7 kilogram na haramtattun ƙwayoyi da suka kai 3 miliyan.”