‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Uba da ‘Da a Babban Birnin Tarayya

 

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani uba da dansa a wani yankin babban birnin tarayya, Abuja.

Rahoto ya bayyana cewa, ‘yan bindigan sun zo su sama da 20 suka yi barna na sama da awa daya.

Yankunan babban birnin tarayya Abuja na ci gaba da fuskantar sace-sacen mutane da harin ‘yan bindiga Wasu.

‘yan bindiga da sanyin safiyar ranar Lahadi sun mamaye yankin Kuchiko a karamar hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya (FCT) inda suka yi awon gaba da wani mazauni da dansa.

Daily Trust ta tattaro cewa ’yan bindigan wadanda yawansu ya kai ashirin sun afka wa yankin, wanda aka fi sani da El-Rufa’i Estate, da karfe 12 na dare kuma suka fara harbi ba kakkautawa.

Bayan sun fi karfin jami’an tsaro, ‘yan bindigan, sun yi amfani da wukake da adduna, suka nufi gidan wanda aka sacen suka yi garkuwa da shi da dan nasa.

An tattaro cewa maharan, wadanda suka yi barna na tsawon awa daya, daga baya sun wuce zuwa gidan wani mazauni kuma suka yi yunkurin sace shi.

Ko da yake, isowar sojoji daga Kwalejin Tsaro ta Bwari a kan lokaci, ya taimaka a halin da ake ciki bayan sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan.

Wasu mazauna yankin, wadanda suka ba da labarin abin da ya faru da su, sun yi kira ga hukumomi da su karfafa tsaro a kewayen yankin.

Jami’in ‘yan sanda na Shiyya a Yankin Bwari (DPO) bai samu damar tabbatar da labarin ba kamar yadda yake a lokacin hada wannan rahoto.

Lamarin sace-sacen mutane na kara yawa a yankunan arewain Najeriya, wanda ya tsoma wasu yankunan babban birnin tarayya Abuja cikin mazan fargaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here