Mutane 64 Sun Jikkata Sanadiyyar Fashewar Tankar Mai a Jahar Kano

 

Rahotanni daga jahar Kano na nuni da cewa aƙalla mutum 64 ne suka jikkata lokacin da wata tankar mai ta fashe a Sharaɗa.

An gano cewa da yawa daga cikin waɗanda abun ya shafa sun zo kallon yadda motar ta faɗi ne kafin daga baya ta fashe.

Hukumar kashe wuta a jahar Kano, ta tabbatar da faruwar lamarin, tace jami’anta takwas na cikin waɗanda abun ya shafa Aƙalla mutum 64 ne sukaji raunuka kala daban-daban bayan wata motar dakon mai ta fashe a jahar Kano.

Daga cikin waɗanda suka samu raunin akwai jami’an hukumar kashe gobara ta jahar Kano waɗanda suka kawo ɗauki cikin gaggawa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka samu raunukan mazaunan unguwar ne. An gano cewa waɗanda suka samu raunin sun zo kallon yadda motar ta faɗi kuma take ci da wuta kafin daga bisa ni ta fashe.

Duk da cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa, amma aƙalla mutum 64 ne suka jikkata kuma yanzun haka suna amsar kulawa a asibitin Murtala dake Kano.

Kakakin hukumar kashe wuta ta jahar, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace jami’an hukumar su 8 na cikin mutum 64 da abun ya shafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here