Zanga-Zanga: ‘Yan Daba Sun Raunata ‘Yan Jarida a Kano

Jihar Kano – ‘Yan jarida a Kano sun shiga barazana yayin da wasu ‘yan daba da su ka shiga rigar zanga-zanga su ka fara tare mutane a Kano.

Ibrahim Ayuba Isa, wanda ya ke dan jarida ne a Kano da ke daukar rahoto kan zanga zanga ga gidan talabijin din TVC ya shaidawa Legit cewa da kyar ya tsira.

Ibrahim Ayuba Isa ya ce ‘yan dabar sun cika mota guda domin daukar labarai a wannan rana, sai ‘yan daba su ka tare su a hanyar Sokoto da ke karamar hukumar Nassarawa inda su ka nemi na goro.

Ya ce gabanin su mika masu wani abu, sai daya daga cikin ‘yan daban ya buga gora ya fasa gilashin motar har ya ji masa ciwo a wuya da hannu.

Masu zanga zanga sun take dan jarida

Ahmad Mahmud, dan jarida da Premier radio ya shaidawa mana cewa ya na cikin tafiya a kokarinsa na zuwa wajen aiki ne wasu masu zanga-zanga su ka yi kansa.

Ahmad Mahmud ya ce daya daga cikin masu zanga-zangar da ke cikin adaidata sahu ne ya yi kokarin bi ta kansa yayin da jami’an tsaro su ka koro su, inda ya ji raunuka.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here