Jihohi 3 da Ƴan Daba Suka Tarwatsa Masu Zaɓe
Rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na cewa ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a sassan ƙasar.
Kano: Wani hoto ya nuna yadda masu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun tarwatsa kayan zaɓe, suka kuma kori jama’a a ƙaramar hukumar Rogo. Lamarin ya faru ne a a lokacin da ake zaɓen gwamnnoni da na ƴan majalisun dokoki.
Lagos: Rahotanni daga kafofin sada zumunta da dama sun nuna cewa an samu tashin hankali a wasu rumfunan zaɓe a cibiyar kasuwancin ƙasar ta Najeriya.
Wata tauraruwar fina-finan Nollywood Chioma Akpotha ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram inda ta yi zargin cewa wasu mutane sun kai mata hari da wuƙa.
Read Also:
“Ban iya ma fito da waya ta ba lokacin da yaran nan suka zo, suka ringa dukan motata, suka fasa min madubin gefe na mota…” tana magana ne a lokacin da take barin rumfar zaɓen.
Bayelsa: Rahotanni na cewa wasu ƴan daba sun kwace tare da lalata kayan zaɓen ɗan majalisar dokoki a rumfuna masu lamba 02 da 03 da 04 da kuma rumfa ta 05 a mazaɓa ta biyar a ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, kamar yadda kafofin yaɗa labarai na jihar suka rawaita.
A nasa ɓangaren, gwamna Douye Diri ya yi Allah wadai da da harin da kakkausar murya, yana mai kira ga babban sufeton ƴan sanda na ƙasa da kwamishinan ƴan sandan jihar Bayelsa su maido da zaman lafiya a yankin, kamar yadda mai taimaka masa a harkokin kafofin watsa labarai Daniel Alabrah ya tabbatar a shafinsa na Faceook.