Ɗaruruwan ‘Yan Gudun Hijira a Najeriya Sun Shiga Halin Ka-ka-ni-ka-yi Kan Barazanar Rasa Matsugunnansu

 

Ɗaruruwan ‘yan gudun hijira da ƴaƴansu a Najeriya sun ce sun shiga halin ka-ka-ni-ka-yi bayan hukumomi sun ba su zuwa yau don su tashi, ko kuma a rusa matsugunnansu a jihar Nasarawa.

Hukumomin dai sun tsugunar da ‘yan gudun hijirar kimanin 1,500 a wani sansani cikin garin Lafia tun a 2004 bayan wani rikicin kabilanci da ya tilasta musu tserewa daga jihar Filato.

Hukumomi sun ce suna kokarin tayar da mutanen ne saboda zargin aikata laifuka, amma ‘yan gudun hijirar sun musanta hakan.

An tsugunar da ‘yan gudun hijirar wadanda suka fito daga Yalwan Shandam na jihar Filato ne, a unguwar Shinge da aka fi sani da unguwar Hijira a yanzu.

Malam Abbas Abdussalam shi ne sakataren kungiyar ‘yan gudun hijirar yace tun da farko da izinin gwamnati suke zaune tun lokacin wurin daji ne kuma yanzu ya zama alkariya hukumomin karamar hukumar Lafiya ke kokarin tayar da su.

Wasu matan masu ƴaƴa da dama sun ce ji suke tamkar yau suka fito gudun hijira.

Shugaban karamar hukumar lafiya Hon. Aminu Mu’azu Maifata ya shaida wa BBC cewa dole ce ta sa za su tashe su, saboda matsalar tsaro.

Kazalika, ya ce sun bai wa ‘yan gudun hijirar notis din su tashi tun-tuni, saboda a cewarsa wurin na karamar hukumar ne.

Bugu da ƙari Honorabul Mai Fata ya ce har wasika suka rubutawa hukumomin jihar Filato ta ofishin sakataren gwamnatin Nasarawa suna shaida musu halin da ake ciki game da ‘yan gudun hijira da suka yi sansani tun 2004.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here