Hukuncin da Kotun Jahar Kwara ta Yanke wa Barawon Doya

 

Wata kotun majistare a jahar Kwara ta yanke wa wani Abubakar Buni daurin watanni shida a gidan yari Alkalin.

kotun ya yanke wa Buni hukuncin ne bayan ya amsa tuhumarsa da ake yi na satar doya daga gonar wasu.

Jami’ian hukumar NSCDC na jahar ne suka gurfanar da shi a kotu bayan wani makwabcinsa ya yi korafi a kansa.

Jahar Kwara – Wata kotun majistare na Jahar Kwara da ke zamanta a Kaiama ta yanke wa wani Abubakar Bani, dan shekaru 28 hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda satar doya.

Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jahar Kwara ne ta gurfanar da Bani saboda satar doya a kauyen Tenebo, a karamar hukumar Kaiama da ke jahar, kamar yadda Nigerian Tribune ta rawaito.

A rahoton LIB, Mai magana da yawun hukumar a jahar, Babawale Afolabi, ya ce wani Ismaila Ebbo Mohammed da makwabtansa da Kibefandi ne suka kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga watan Agustan 2021, misalin karfe 6 na safe.

Ya ce:

“A cewar wadanda suka kai korafin, bafulatanin ya dade yana zuwa satar doya a gonar a kowanne rana. Wanda ake zargin, Abubakar, ya amsa cewa ya aikata laifin kuma nan take kwamandan NSCDC na jahar Kwara, C.C. Makinde Iskil Ayinla, ya bada umurnin a gurfanar da shi a kotu.”

Jami’in hulda da jama’an ya kara da cewa:

“An gurfanar da Abubakar Bani a kotun Majistareda ke Kaiama nan take, tunda wanda ake zargin ya amsa laifinsa. Don haka Alkalin Kotun, Yusuf Kide, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali na New Bussa jahar Niger bisa laifin kutse da sata.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here