Ƴan Najeriya 64.3m ne Ke Fama da Yunwa – MDD

 

Ƴan Najeriya miliyan 64.3 ne aka kiyasta cewa suna fama da matsalar ƙarancin abinci, a cewar Hukumar Samar da Abinci ta Duniya.

Hukumar ta ce mutum miliyan 170 a faɗin ƙasashe 19 ba su da isasshen abinci.

Ƙasashen da suka fi fuskantar matsalar sun haɗa da Niger da Mali da Burkina Faso da Guinea da Chadi da Saliyo da Kamaru da Liberia da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Togo da Guinea Bissau da kuma Najeriya.

A wani rahoto da hukumar ta fitar kan ƙarancin abinci, ta ce ƙarancin abinci a Najeriya ya ƙaru daga kashi 29 zuwa 32 a cikin watanni uku da suka wuce.

Ta ce matsalar ƙarancin abinci da ci-maka a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka ta yamma na kawo cikas na kyakkyawar rayuwa ga al’ummomin ƙasashen da dama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com