Mutane 5 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyar Hatsarin Mota a Jihar Bauchi

 

Hukumar kiyaye haɗura reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutum biyar da suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos kusa da ƙauyen Panshanu.

Hukumar ta ce hatsarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya Laraba bayan da wata mota ƙirar Toyota ta gamu da ta Peugeot waɗanda duka ke ɗauke da fasinjoji a cikinsu bayan da motar ta kuɓcewa ɗaya daga cikin direbobin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maza biyar da ke cikin motar duk sun mutu bayan da suka ƙone kurmus saboda kama da wuta da motocin suka yi.

An mika gawarwakin mutanen tare kuma da motcin zuwa hannun hukumar ƴan sanda shiyyar Toro da ke jihar ta Bauchi.

Haka-nan ma a jihar Kebbi, mutum 35 ne suka rasa rayukansu a ranar Laraba a wasu haɗura biyu da suka afku tsakanin 26-27 ga watan Maris, a cewar hukumar kiyaye haɗura a jihar.

Babban kwamandan hukumar a jihar, Yusuf Haruna Aliyu, ya ce an samu nasarar ceto mutum 40 daga haɗarin. Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wasu motoci guda uku waɗanda ke ɗauke da mutum 75 a cikinsu.

Ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Jega da kuma Kalgo.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com