Gidan Bauta ya Rufta da Mutane a Indiya

 

Ƴan sanda na can suna kokarin kuɓutar da masu bauta da suka rufta a wani wurin bauta a yankin Madhya Pradesh da ke Indiya.

Mutane sun taru a wurin ne domin yin wani biki da aka saba yi mai suna Ram Navami.

Gidan bautan ya rufta ne bayan cikar da mutane suka yi a wurin, inda aka fitar da mutum takwas da suka faɗa cikin ruwa zuwa asibiti.

Kamfanin Dillancin Labaran ANI, ya ruwaito cewa tuni gwamnati ta soma gudanar da aikin ceto a wurin.

Babban ministan yankin Shivraj Singh Chouhan ya bayar da umarnin cewa a gaggauta aikin ceto domin fitar da mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Ya ce yana magana da hukumomi a yankin na Indore don ganin aikinya tafi cikin sauri.

Mutane da lamarin ya faru a idonsu sun ce gwamman mutane ne suka rufta waɗanda galibi suka je don yin biki a wurin bautan.

 

 

hoth guest post

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com