Sojoji na Fama da ƙarancin abinci: Rundunar Tsaron Botswana ta Musanta Rahoton

 

Rundunar tsaron Botswana ta musanta rahotannin da ke cewa sojojinta da aka tura zuwa arewacin Mozambique domin aikin wanzar da zaman lafiya na fama da matsalar ƙarancin abinci.

Sojojin sun musanta rahoton da wata jarida ta wallafa, inda ta ce ba shi tushe balle makama.

A cikin wata sanarwa da rundunar tsaron kasar ta fitar a ranar Laraba, ta ce ana bai wa sojojinta da ke yankin Cabo Delgado duk irin kulawar da ta kamata don samun ƙwarin gwiwar fafatawa da su.

Dakarun Botswana kusan 300 ne aka tura zuwa Mozambique a 2021 karkashin wani shiri na ganin ci gaban al’ummomi a yanin kudancin Afirka.

Kafafen yaɗa labaru sun ce aikin samame da sojojin Mozambique da na Samim ke yi, ya janyo raguwar ayyukan mayaƙa a arewacin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com