Amurka ta ƙara Kuɗin Shiga ƙasarta

 

Amurka ta ƙara yawan kuɗin da take karɓa daga masu neman takardar izinin shiga ƙasar ga masu son zuwa yawon buɗe ido da kuma karatu.

A wata sanarwa ta ma’aikatar hulɗa da ƙasashen wajen Amurka, ƙasar ta ƙara yawan kuɗin masu neman takardar shiga ƙasar zuwa dala 185 daga 160.

Sanarwar da aka wallafa ranar 28 ga watan Mayu ta ce ƙarin zai fara aiki ne daga yau 30 ga watan Maris, 2023.

Haka nan an yi ƙarin kuɗin a kan masu neman takardar shiga ƙasar domin waɗansu abubuwan na daban, kamar aikin da kuma masu zuba jari.

Amurkar ta ce ta yi hakan ne domin inganta yadda take bayar da takardar shiga ƙasar ga baƙi da kuma ƴan ci-rani.

Kuma sanarwar ta ce an yi ƙarin ne ta hanyar la’akari da kuɗin da ake kashewa wajen samar da takardun.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com