Motar Gidan Yari ɗauke da Fursunoni ta Haddasa Hatsari a Jihar Osun

 

Osun – An shiga yanayin tashin hankali da ɗar-ɗar a Osogbo, babban birnin jihar Osun ranar Alhamis yayin da wata motar gidan Yari ta haddasa hatsari a kan Titi.

Punch ta tattaro cewa motar wacce ke ɗauke da Fursunoni zuwa babbar Kotun jiha, ta bugi wata ƙaramar motar haya, lamarin da ya yi sanadin raunata mutum biyu.

Wani ganau da abun ya faru a kan idonsa ya ce Direban motar gidan gyaran halin ne ya ƙi bin Fitilar da ke baiwa matafiya hannu a kan Titin.

Ya ce sanadin haka ne Direban motar da ta ɗauko Fursunonin ya bugi ƙaramar Motar Bas ta haya, Direba da fasinja ɗaya suka jikkata sakamakon haka.

Nan take lamarin ya haddasa zanga-zanga, inda direbobin motocin haya da wasu fusatattun matasa suka toshe babbar mahaɗar titunan Olaiya Junction da sunan zanga-zanga.

Zuwa yanzun da muke haɗa maku wannan tarohon, jami’an rundunar ‘yan sandan da suka kai ɗauki wurin da lamarin ya faru sun tarwatsa masu zanga-zanga.

Ƙarin bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com