‘Yan Najeriya Miliyan biyu za su Fara Karbar N5000 Daga Watan Yuni – Gwamnatin Tarayya

 

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ‘yan Najeriya miliyan biyu za su fara karbar Naira dubu biyar-biyar daga watan Yuni, a matsayin tsabar ƙudi na yau da gobe dana tsarin conditional cash transfer wanda ke karkashin shirin National cash transfer program.

An tattaro cewa gwamnatin tarayya za ta biya su Naira dubu biyar 5,000 ga kowannen su, saboda haka aka ware naira biliyan ashirin domin kashe su a wannan fannin ga waɗanda zasu ci gajiyar shirin, musamman talakawa da masu rauni.

Daftarin watan Maris kan taswirar ayyukan Ma’aikatar Jin kai, Agaji da inganta rayuwar al’umma ta Tarayya, ya nuna cewa adadin masu cin gajiyar shirin yana ta karuwa.

Takardar ta bayyana cewa a shekarar 2018, jihohi 19 ne ke karkashin shirin, na National cash transfer program wanda suka karu zuwa jihohi 24 a shekarar 2019, ya sake karuwa zuwa jihohi 36 da babban birnin tarayya a shekarar 2022, wanda ya kunshi kimanin mutane miliyan 1.6.

Kuma, ministan kula da harkokin jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma, Sadiya Umar Farouq ta bayyana a cikin takardar, cewa adadin zai karu a watan Yuni,

rike makarantu, kyakkyawan ruwa da yanayin tsafta a muhallinsu/gidajensu,” in ji ministan.

Ministan ta bayyana cewa ma’aikatar ta tsara tare da yin gwajin wani rijistar zamantakewa mai suna Rapid Response Register, don samo ma’aikata marasa galihu a birane, waɗanda ke karbar albashi na yau da kullun a garuruwa dama birane waɗanda cutar COVID-19 lockdown ya shafa.

“Kawo yanzu, cikin wannan miliyan dayan da gwamnatin ta yi niyya, mun biya dubu biyar-biyar ga masu cin gajiyar shirin, mutane 850,000 ta hanyar dijital ta hanyar Inter-bank Settlement System Na Najeriya inda kowane asusu sai da aka tantance su a tsanake kafin aka biya.

“Za a biya mutane 150,000 a karshen watan Afrilu. Kowanne daga cikin waɗannan masu cin gajiyar shirin suna karbar tallafin watanni shida ne a tsabar kudi,” in ji ta

Ma’aikatar ta ce a karkashin National social register na kasa, mutane miliyan 46 a cikin jihohi 36 da birnin tarayya, waɗanda suka kunshi gidaje miliyan 11, sun yi rajista na shekarar 2022.

Ta kara da cewa shirin na N-Power ya samar da guraben aiki na wani dan takaitaccen lokaci ga mutum 498,602 wanda suka kammala cin gajiyar shirin a karkashin Rukunin A da B yayin da 450,000 da suka kammala jin gajiyar shirin a karkashin Rukunin C.

an kuma haɗa da yan Stream 1.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa akwai wasu 390,000 da ke cikin shirin na Batch C Stream 2 kuma akwai amincewar shugaban kasa kan cewa a shigar da karin mutane miliyan daya waɗanda zasu amfana.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here